Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Ana zanga-zangar adawa da manufar Rasha akan Crimea a Moscow

A kasar Rasha, dubban mutanen kasar sun fito saman tituna a birnin Moscow suna zanga-zangar adawa da manufar Gwamnatin Rasha a kan yankin Crimea a kasar Ukraine, inda a gobe Lahadi mutanen yankin na Crimea ake sa ran zasu kada kuri’ar komawa karkashin ikon Rasha ko ci gaba da zama a cikin Ukraine.

Dubban Mutanen dauke da Tutar Rasha da Ukraine suna zanga-zangar adawa da manufar Rasha akan Crimea
Dubban Mutanen dauke da Tutar Rasha da Ukraine suna zanga-zangar adawa da manufar Rasha akan Crimea REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun fito ne dauke da tutar Rasha da Ukraine kuma suna yayata kalaman adawa daidai da na mutanen Ukraine da suka kai ga hambarar da gwamnatin Viktor Yanukovych mai ra’ayin Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.