Isa ga babban shafi
Rasha-Syria

Rasha zata hau kujerar na-ki akan Syria

Kasar Russia tace za ta hau kujerar na-ki idan kwamtin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zo tattaunawa, game da kudirin da ke nema a shigar da kasar Syria kara a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC. A cewar Jakadan Rasha da ke kwamitin, gabatar da rikicin na Syria a gaban kotun, zai raunana kokarin da ake yi na neman mafita ga rikicin siyasar kasar.

Talla

A yau Alhamis ne ake sa ran mambobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, za su kada kuri’ar amincewa ko akasin haka kan wannan kudiri, da kasar Faransa ta gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.