Paparoma Francis na ziyara a kasashen Gabas ta Tsakiya
Jagoran mabiya mujami’ar Katolika na Duniya Paparoma Francis na daya, a yau asabar ya isa kasar Jordan, wato matakin farki na ziyarar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da zummar kara samar da hadin kai tsakanin mabiya addinan Kirista, Yahudawa da kuma Musulmi.
Wallafawa ranar:
Paparoma Francis, wanda ke gabatar da jawabi a birnin Amman, ya bukaci a kawo karshen yakin basasar kasar Syria, sannan kuma a gaggauta samar da dawwamammen zaman lafiya tsakanin Isra’ila da kuma alasdinu.
Bayan ganawarsa da hukumomin kasar ta Jordana yau, an tsara jagoran na cocin Katolika zai gana da dubban ‘yan gudun hijirar kasar Syria da ke zaune a kasar ta Jordan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu