Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

An kirkiro ma'aikatar kudi a fadar Paparoma ta Vatican

Paparoma Francis ya kirkiro sabuwar ma’aikatar kudi, da za ta rinka sa ido kan harkokin kudi da tatalin arzikin fadar. Fadar ta Vatican tace ta dauki wannan matakin ne don tallafawa talakawa da kuma kashe kudi kan ka’ida.Wani limanin darikar katilika dan kasar Australiya mai suna George Pell ne zai jagoranci ma’aikatar kudin, da za ta rinka shiryawa fadar Vartican kasasfin kudi duk shekara, tare da tabbatar da cewa an bi dokokin kudi na duniya sau da kafa.Fadar ta Vatican tace an dauki matakin kirkokro da ma’aikatar ne, sakamakon bukatar yin hakan da wani gungun Limaman darikar ta Katolika suka yi ta mika wa Paparoma.Cikin dokar daya kaddamar Paparoma Francis ya amince da babban bankin Vatican, da zai rinka hulda da sauran manyan bankunan kasashe.Paparoma ya kuma ce yana fatan ganin an fitar da wani tsarin na cude ni in cude ka, maimakon fadar ta zama mai wuka da nama.Wasu na ganin Sanarwar a matsayin wani mataki, kan kokarin Paparoma yin a neman kawo sauye sauye a majalisar gudanarwan fadar.An kuma nemi shawarawri daga wasu daga wajen fadar, inda aka yi hayar kwararru, da za a dama da su. 

Paparoma Francis
Paparoma Francis
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.