Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Paparoma ya nemi a kaswo karshen tashe tashen hankula a duniya

Shugaban mabiya darikar Katolika a duniya Paparoma Francis na daya, ya bukaci a samar da zaman lafiya da kuma kyakkyawar alaka a tsakanin mabiya addinai a sassa daban daban na duniya, musamman inda ake fama da rikice-rikice. A sakonsa da ya aike wa mabiyansa dangane da zagayowar ranar Easter, Paparoma Francis ya ce bai kamata kasashen duniya su zura ido ana ci gaba da zubar da jini a kasashen Syria, Iraki, Libya, Yemen da dai sauransu ba.Paparoma Francis ya ce yama mai fatan samun zaman lafiya musamman ma a kasashen Syria da Iraki, fatan da yake da shi a game da wadannan kasashen shi ne kawo karshen zubar da jini da kuma dawo da kyakkyawar alaka tsakanin mabiya addinai mabambanta a yankin.Shugaban na mabiya darikar Katolika yace, yana fatan ganin irin wannan zaman lafiya tsakanin Palasdinawa da Yahudawan Isra’ila, da kuma kasar Libya wadda a yau ke fama da zubar da jini.Paparoma yace yana kira ga duk wadanda ke da hannu a wannan rikici na Libay, da su warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar sulhu.Daga karshe yace abin da ke faruwa a kasar Yemen shi ma wani babban bala’i ne da bai kamata a zura ido yana ci gaba da faruwa ba, inda kuma yayi fatan Ubangiji Allah ya dora duniya akan hanya mafi a’ala, da za ta kai ga samar da zaman lafiya da kuma cudayya a tsakain al’umma.  

Paparoma Francis yana jawabi ga magoya bayan shi
Paparoma Francis yana jawabi ga magoya bayan shi REUTERS/Alessandro Bianchi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.