Isa ga babban shafi
Amurka-Koriya

Amurka ta gargadi korea ta arewa kan kallaman tsokanan

Amurka ta yi kira ga korea ta Arewa cewa ta daina amfani da kallaman tsokanan a wata sanarwar da ta fitar domin kaucewa haifar da rikici a yankin gabashin Asiya.

路透社
Talla

Mai magana da yawun fadar white house Josh Earnest ne ya fitar da sanarwa bayan Koriya ta arewa ta ce tana inganta yadda ta ke kera makaman ta na nukiliyar domin fara kai wa Amurka hari da su.

Batun da ake ganin cewa Koriya ta arewa ta sanar da haka ne domin ta nuna wa duniya cewa tana da karfin soji.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan kasar ta ce tana shirin kaddamar da wadan su taurarin dan adam domin kai harin roka a dogon-zango.

Wasu hotunan tauraron dan adam da aka fitar a makon jiya sun nuna yadda ake ci gaba da ayyukan a yankunan da ake kera makaman nukiliyar Koriya ta arewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.