Isa ga babban shafi
Mexico-Egypt

Mexico ta bukaci bincike kan Mutuwar ‘yan kasar ta a Masar

Minister harkokin wajen kasar Mexico Claudia Ruiz Massieu ta bukaci hukumomin Masar su gudanar da bincike mai zurfi kan mutuwar ‘Yan kasarta masu yawon bude ido da jami’an tsaron Masar suka kashe ta hanyar kaddamar musu da hare haren sama.

Ministar harkokin wajen Mexico Claudia Ruiz Massieu
Ministar harkokin wajen Mexico Claudia Ruiz Massieu AFP/AFP
Talla

Ministar ta bukaci haka ne a lokacin da ta ziyarci birnin Alkahira na Masar domin duba lafiyar 'yan Kasar ta Mexicio da ke kwance a Asibitin Dar Foud bayan sun jikkata a hare-haren da jami’an Suka kaddamar musu a yammacin Saharar Masar.

Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar 'yan Mexico 8 daga cikin masu yawon bude idon da farmakin ya ritsa da su, to sai dai hukumomin masar sun ce, an kashe mutanen ne cikin kuskure bayan motocin da ke dauke da su sun biyo ta hanyar da Jami’an tsaron ke aikin farautar mayakan Jihadi, kuma da dama dai an haramta bin hanyyar.

Tuni dai hukumomin suka bayyana cewa suna kan gudanar da bincike kan lamarin yayin da ake sa ran Minsitar zata gana da shugaban Kasar Masar Abdel Fatah Alsisi bayan ta kammala duba lafiyar yan Kasarta

A wata wasika da ya aikewa hukumomin Mexico a jiya talata, Ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya bayyana rashin dadinsa da aukuwar lamarin tare da yin ta’aziya ga ‘yan uwan wadanda farmakin ya ritsa da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.