Isa ga babban shafi
Saudi-Arabia

Al-ummar Musulmi sun fara aikin hajji a Saudiya

A yau Talata Maniyatta aikin hajji daga sassan daban-daban dake saudiya za su tafi Minna domin fara gudanar da aikin hajji kamar yadda aka saba a kowacce shekarar. 

Flickr user 'transposition'
Talla

Kimanin mutane miliyan 2 ne ake sa ran za su sauke farali a wannan shekarar kuma miliyan 1.4 daga cikinsu baki ne daga kasashen duniya yayin da kuma dubban al-ummar  Saudiya suma suka shiga sahun Mahajjatan.

Kasar Indonesia wadda tafi yawan musulmai a duniya na da Mahajjata dubu 168 kuma kashi 80 cikin 100 na daukacin Mahajjatan wannan bana sun isa Saudiya ne ta hannun hukumomin kasashensu, inda kuma kashi 20 suka isa ta hannun kamfanonin jiragen yawo.

Tuni dai mahukuntan Saudiya suka girke Jami’an Yan Sanda dubu 100 domin samar da tsaro ga Mahajjatan.

Har ila yau, Ma’aikatar lafiyar Sudiya ta tanadi Jami’an kiwon lafiya dubu 25 domin kula da Mahajjatan da kan iya gamuwa da rashin lafiya a lokacin aikin hajjin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.