Isa ga babban shafi
Birtaniya

Dubban mutane sun yi zanga zanga a Birtaniya

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga zanga a Birtaniya domin nuna kiyayarsu da shirin gwamnatin kasar na shiga yakin da ake yi  da kungiyar ISIS a kasar Syria.

Firaministan Birtaniya David Cameron a zauren majalisar dokokin kasar.
Firaministan Birtaniya David Cameron a zauren majalisar dokokin kasar.
Talla

Yau ake sa ran Majalisar kasar za ta tafka mahawara na sa’oi 10 don amincewa ko kuma watsi da bukatar Firaminista David Cameron na amfani da sojojin kasar don kai hare haren sama cikin kasar Syria.

Cameron ya ce kaddamar da hari a Syria kan mayakan ISIS shi ne zai hana su kai wa Birtaniya hari kamar yadda suka yi a birnin Paris na Kasar Faransa, inda suka kashe mutane 130 tare da jikkata wasu da dama.

To sai dai masana harkar tsaro da 'yan majalisu da kuma jama’ar kasar da dama ba sa goyan bayan shirin gwamanatin kasar ta Birtaniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.