Isa ga babban shafi
Ukraine

Merkel da Hollande da Putin da Poroshenko sun jaddada matsayinsu kan Ukraine

Shugabannin kasashen Jamus da Faransa da Rasha da Ukraine sun sake jaddada goyon bayansu ga yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Ukraine a yau Laraba bayan sun tattauna ta wayar wayar tarho.

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus da Rasha suna tattaunawa kan rikicin Ukraine
Shugabannin kasashen Faransa da Jamus da Rasha suna tattaunawa kan rikicin Ukraine REUTERS/Ukrainian Presidential Press Service/Mikhailo Palinchak
Talla

Shugaba Francois Hollande, na Faransa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Ukraine Petro Poroshenko sun amince da matakin tsagaita wutar a gabashin Ukraine bayan sun shafe sa’o’I biyu suna tattaunawa ta wayar tarho.

Wannan ne karon farko da shugabannin suka gana tun taron Paris a ranar 2 ga watan Oktoba.

Sanarwar da fadar gwamnatin Faransa ta fitar tace shugabannin sun amince a gaggauta ficewa da manyan makamai a yankin.

Shugabannin sun jaddada bukatar amfani da yarjejeniyar Minsk da aka amince kan rikicin Ukraine da ta kunshi gudanar da zaben kananan hukumomi a farkon 2017 a gabashin Ukraine.

Gwamnatin Faransa ta ce nan gaba a watan Fabrairu ne ministocin harakokin wajen kasashen hudu zasu gudanar da taro domin tattauna makomar Ukraine.

Rikicin Ukraine dai ya laukume rayukan mutane kusan 10,000, inda aka rusa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince a watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.