Tarayyar Turai ta tsawaitawa Rasha takunkumi
Kungiyar Tarayyar Turai ta tsawaita takunkuman kariyar tattalin arziki da ta kakaba wa Rasha sakamakon rawar da kasar ke takawa a rikcin Ukraine.
Wallafawa ranar:
Mambobin Kasashe 28 a majalisar kungiyar wadanda suka gudanar da taro a birnin Brussels, sun ce Rasha ta ki mutunta yarjejeniyar sulhun da aka kulla tsakaninta da Ukraine da kuma ‘yan aware a birnin Minsk domin kawo karshen wannan rikici, saboda haka ya zama wajibi a tsawaita takunkuman da aka sanya wa kasar.
Kungiyar Turai ta ce ta lura shekara ta 2015 na gaf da kawo karshe ba tare da Rasha ta canza matsayi a game da irin rawar da ta ke takawa a gabashin Ukraine ba, kuma a irin wannan yanayi ba makawa face tsawaita takunkuman karya tattalin arziki a kanta.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar jim kadan bayan sanar da matakin na Tarayyar Turai, ma’aikatar harkokin wajen Rasha, ta bayyana takaicinta a game da yadda kungiyar ta kawar da kai a game da matsalar ta’addanci wadda ita ce babbar barazana a cewarta, inda a maimakon haka Turai ta zabi tsawaita takunkuman.
Kafin nan dai Firaministan Rasha Dmitry Medvedev, ya ce za su tsawaita takunkumai na tattalin arziki a kan kasar Ukraine saboda kasar ta zabi yin huldar kasuwanci da Turai a maimakon Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu