Isa ga babban shafi
WHO-Zika

WHO ta gayyaci taron gaggawa kan Zika

Hukumar Lafiya ta Majalisar dinkin duniya ta kira taron gaggawa a ranar litinin mai zuwa a birnin Geneva, domin tattauna wa kan Cutar Zazzabin Zika dake yaduwa a yankunan Amurka da sassan Turai.Inda ta bayyana furgaban makomar miliyoyin al’ummar muddin ba a dauki matakan gaggawa ba.

Shugabar Hukumar Lafiya ta MDD Margaret Chan
Shugabar Hukumar Lafiya ta MDD Margaret Chan REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Shugabar Hukumar Lafiya ta MDD Margaret Chan ta ce sun kafa Kwamiti na musamman da za suyi wannan zama don duba matakan da ya dace a dauka a hukumance wajen hana yaduwar kwayar cutar Zika da ke haddasa haihuwar jarirai da nakasa.

Chan ta ce cutar da sauro ke hadasawa ta ba zu a kasashe 23 na Turai inda a brazil kawai mutane 163 ke dauke da ita kuma ta yiwa jarirai 68 yanzu illa.

Kasashe irin su Colombia, Ecuador, El Salvador, Jamaica da Puerto Rico sun gargadi matansu kan samu ciki a wannan lokaci, yayin da Faransa ta bukaci matan kasar su dakatar da tafiya kasashen waje irinsu Yankin kudanci Amurka da Caribbean.

Chan ta shaidawa Mambobin Hukumar lafiya cewa yanayi yaduwar kwayar cutar na da tada hankali, kuma lura da yaduwar sauro a yankunan da dama dole a yi taka tsan-tsan

Ko a shekarar 1947 da cutar da bula a Uganda ba ta yi barna kamar wannan lokaci ba da ta ke neman zama annoba, lura da yaduwar ta tamkar wutar daji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.