WHO ta kaddamar da dokar ta-baci akan Zika
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta kaddamar dokar ta-baci domin dakile yaduwar Cutar Zika da ta fi yin illa ga jarirai wadanda ake haifuwa da karamin kai.
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya dai na fuskantar matsin lamba ne kan gano illolin cutar da hanyoyin magance ta, a yayin da ta ke ci gaba da fama da cutar Ebola a kasashen Afrika.
Ana kamuwa da Cutar Zika ne daga cizon sauro kuma yanzu dubban mutane ne cutar ta shafa a watannin da suka gabata a kasashen Latin Amurka.
Tuni dai Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa za a samu karuwar masu kamuwa da cutar a bana wanda ya zama wajibi a dauki matakan dakile yaduwarta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu