Isa ga babban shafi
WHO-ZIKA

MDD na son a daina haihuwa saboda Zika

Majalisar dinkin duniya ta bukaci kasashen da aka samu bullar cutar zazzabin Zika da su bai wa mata damar amfani da kwayoyin hana haihuwa da kuma damar zubar da ciki don kaucewa haihuwan yara masu nakasa.

Zika na haddasa haihuwar yara masu matsalar kwakwalwa
Zika na haddasa haihuwar yara masu matsalar kwakwalwa REUTERS/Alvin Baez
Talla

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar ta ce, hana mata daukar ciki da wasu kasashen da ke fama da cutar suka yi, bai wadatar ba, ya kamata a bai wa matan zabi na amfani da kwayoyi ko matakin zubar da cikin kafin ko bayan sun samu juna biyu a lokacin wannan annoba.

Tun bayan bullar zazzabin Zika a wasu kasashen duniya ne aka soma bai wa mata shawarar kaucewa daukar ciki don hana su haihuwar yara masu kananan kai ko nakasa

Ana dai ci gaba da kokarin ganin an dakile yaduwar wannan cutar ta Zika a duniya baki daya wadda sauro ke yada kwayarta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.