Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta kashe mayakan al-Qaeda 40

Kasar Amurka ta hallaka mayakan al-Qaeda 40 a hare hare da ta kaddamar kan sansaninsu inda su ke atisaye a kudu maso gabashin Yemen kamar yadda jami’an gwamnatin da ke yankin su ka tabbatar.

Jiragen yakin Amurka
Jiragen yakin Amurka REUTERS/Han Jae-Ho
Talla

Amurka ta kaddamar da hare haren saman ne a sansanin Hajr da ke yammacin lardin Hadramwat a birnin Mukalla tare da jikkata mayakan da dama.

Ma’aikatar tsaron Pentagon ta kuma sanar da tarwatsa duk wani waje a yankin da mayakan ke amfani da shi wajen kai hare haren ta’addanci.

Wani mazaunin yankin da lamarin ya auku ya ce tabbas Amurka ta kashe mayakan al-Qaeda da dama a sansanin da su ke bai wa sabbin mambobinsu horo, sai dai kuma akwai wadanda su ka tsira da ransu, sannan suka sake bazuwa a sabbin wurare.

Tun a watan Afrilun bara mayakan al-Qaeda ke iko da Mukalla da mafi yawa daga cikin yankunan Hadramwat.

Al-Qaeda na amfani da damar da ta ke samu a yakin Saudiya da ‘yan tawayen Huthi wajen mamaye yankunan Yemen da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.