Isa ga babban shafi
Panama

Ana mayar da martani kan tonon asirin Panama

Fadar shugaban Rasha Vladimir Putin ta mayar da zazzafan martani a game da bayanan sirrin da aka wallafa da ke zargin shugaban da kuma shugabannin kasashen duniya da dama da rashawa ta bilyoyin kudade.

Kwarmaton Panama ya shafi shugabannin duniya da dama
Kwarmaton Panama ya shafi shugabannin duniya da dama DR
Talla

Wasu Takardun bayanan asiri da aka fitar daga Panama sun nuna cewar manyan ‘yan siyasar duniya, da wasu fitattun mutane na boye tarin dukiyarsu a kasar don kaucewa biyan haraji da kuma halatta kudaden haramun.

Cikin wadanda ake zargin sun hada da shugaban Rasha Vladimir Putin da Firaministan Pakistan da Sarki Abdallah na Saudiya da shuagaban China, da Firaministan Birtaniya David Cameron

Sannan akwai Lionel Messi gwarzon dan wasan kwallon kada na duniya, da dan wasan fim Jakie Chan.

Rahoton binciken wanda wata cibiya da ke kasar Panama ta fitar, ya dogara ne a kan wasu muhimman bayanai na sirri sama da milyan 11, inda a ciki aka ambaci manyan kamfanoni na kasashen duniya akalla 35, bankuna sama da 500 da shugabannin kasashen duniya ciki har da na Afrika da halasta kudaden haram da kuma rashawa.

Sai dai wadanda aka ambata a rahoton na tonon asiri sun fara mayar da martani.

Fadar Gwamnatin Rasha da iyalan gidan Firaministan Pakistan da Lionel Messi sun yi watsi da zargin wanda suka karyata tare da kare kansu.

wannan kwarmaton na Panama dai ya kasance mafi girma fiye da tonon asirin da Shafin Wikileaks ya yi a can baya.

Binciken na Panama dai ya shafi kasashe da dama ciki har da Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.