Isa ga babban shafi
Faransa-Masar

Masar ta nemi Faransa ta ba ta bayanai kan EgyptAir

Mai shigar da kara na gwamnatin Masar, Nabil Sadek ya bukaci takwaransa na Faransa da ya bayar da bayanai kan jirgin EgyptAir da ya yi hatsari a tekun Bahru-rum bayan ya taso daga Paris a makon jiya dauke da mutane 66.

Jirgin EgyptAir na Masar
Jirgin EgyptAir na Masar Reuters
Talla

Mr. Sadek na bukatar a mika ma sa takardu da hotunan bidiyo da sautin muryoyin da aka nada gabanin tashin jirgin daga filin jiragen sama na Charles de Gaulle.

Hukumomin Masar sun ce, matukan jirgin ba su kira su ba ta wayar sadarwa gabanin bacewarsa, yayin da hukumomin Girka suka ce, sun zanta da matukan jirgin a lokacin da ya shiga sararin samaniyar kasar kuma a wannan lokacin, jirgin na cikin koshin lafiya.

Wannan ne yasa Masar ta sake bukatar hukumomin Girka da su ba ta bayanai kan hirar da suka yi da matukan.

An daina jin duriyar jirgin ne bayan ya shiga sararin samaniyar tekun Bahru-rum a ranar Alhamis din da ta gabata kuma an yi amanna cewa, dukkanin mutanen cikin sa sun riga mu gidan gaskiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.