Isa ga babban shafi
US

Shahararren Dan Dambe Mohamed Ali Ya Rasu

Shahararren dan damben na duniya  zamani Mohamed Ali ya rasu Juma'a yana da shekaru 74 a duniuya, kamar yadda wata sanarwa da sa hannun mai Magana da yawun dangi da ‘yan uwan sa Bob Gunnell ke cewa.

Marigayi Mohamed Ali a shekara ta 2011.
Marigayi Mohamed Ali a shekara ta 2011. rfi
Talla

Marigayi Mohamed Ali ya yi fama da cutar makyarkyatan jiki mai suna Pakinson na tsawon shekaru 32 wadda ake danganta ta da irin duka da aka rika yiwa fuskar sa.

Ya rike kambun wannan dambe na duniya na tsawon shekaru samada 30, ana karawa dashi yana samun nasara.

A wannan mako aka kwantar dashi a wani asibiti dake Phoenix, Arisona saboda laulayi a makogoron sa.

Sunan san a ainihi shine Cassius Clay kafin shekara ta 1964 ya koma Mohamed Ali bayan ya musulunta
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.