Za a gyara akwatin nadan bayanan EgyptAir a Paris
An isar da akwatin nadan bayanai na jirgin kasar Masar EgyptAir da ya hatsari teku zuwa birnin Paris na Faransa domin gayara shi saboda matsalar da ya samu, abinda ya hana hukumomi samun bayanan da ke ciki don gano musabbabin aukuwar hatsarin jirgin wanda ya taso daga Faransa.
Wallafawa ranar:
Kakakin hukumar binciken hadarin ya ce, an kai na’urar ne don gyara ta, ganin lalacewar da ta yi ta yadda ba za a iya fitar da bayanan dake cikinsa ba.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da alkalan Faransa ke kaddamar da bincike sakamakon mutuwar 'yan kasar 15 a cikin jirgin mai dauke da fasinjoji 66.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu