Har yanzu Kungiyar IS barazana ce ga Duniya-Obama
Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya ce duk cewa rundunar soji ta hadin gwiwa da kasarsa ke jagoranta na samun nasara kan kungiyar IS, har yanzu mayakan barazana ne ga zaman lafiyar duniya.
Wallafawa ranar:
Obama ya bayyana haka ne yayin wani taro da manyan jami’an gwamntinsa a Pentagon, inda suka tattauna batun kananan hare-hare da wasu tsirarun mutane ke kaiwa kan jama’a musamman a nahiyar turai.
Shugaban Amurkan ya ce tilas ne kasar ta yanke duk wata kafar sadarwar kungiyar ta IS da rassanta a sassan duniya, don dakile tasirin da sakwanninta ke yi wajen haifar da ta’addanci kan jama’a.
A baya kungiya IS ta sha daukar alhakin wasu hare-haren ta’addanci da aka kai kan mutane daga ciki akwai wadanda aka kai a birnin Nice na kasar Faransa, Orlando da kuma na Florida a kwanannan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu