Isa ga babban shafi
Jamus

Mutane da dama sun mutu a harin Munich

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani katafaren shagon siyan kayayyakin masarufi da ke birin Munich na kasar Jamus.

Jami'an tsaron Jamus sun yi wa shagon da aka kai hari a Munich kawanya
Jami'an tsaron Jamus sun yi wa shagon da aka kai hari a Munich kawanya Matthias Balk / dpa / AFP
Talla

Jami’an ‘yan sandan kasar sun ce, wasu mutane uku ne dauke da makamai suka kaddamar da harin a yau jumma’a.

Sai dai kawo yanzu an gaza kayyade hakikanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu amma ana ganin akalla ba za su gaza shida ba.

Jaridar Bild ta Jamus ta rawaito cewa, an hangi daya daga cikin maharan na bude wuta ba tare da kakkautawa ba a katafaren shagaon wanda ke kusa da filin wasannin Olympics kafin daga bisani ya ruga ta hanyar wata tashar jirgin kasa.

Tuni dai jami’an ‘yan sanda suka yi wa shagon kawanya, baya ga jirgin sama mai saukar ungulu da ke shawagi a sararin samaniya.

Tun lokacin da wani matashi ya kai harin wuka kan fasinjan jirgin kasa a Bavaria a ranar Litinin, jami’an tsaron Jamus ke cikin shirin ko-ta-kwana.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi alkawarin nuna goyon baya ga Jamus kan wannan harin da ake ganin na ta’addanci ne.
 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.