Isa ga babban shafi
Brazil

Rousseff ta roki kar a tsigeta

Shugaban kasar Brazil dake fuskantar dakatarwa Dilma Rousseff ta bayyana gaban Majalissar Dattijen kasar domin kare kanta daga yunkurin tsigeta. Rousseff ta bayyana tsigeta a matsayin Juyin Mulki.

Shugaba Dilma Roussef na kare kanta a gaban Majalisa
Shugaba Dilma Roussef na kare kanta a gaban Majalisa EVARISTO SA / AFP
Talla

A wani jawabinta kafin soma mata tambayoyi, Rousseff, tace ta bayyana ne yau domin sake jadada cewa bata aikata laifin da ake zarginta ba don haka kar a amince da batun tsigeta.

Majalissar zata yiwa Rousseff tambayoyi, kafin gobe talata ko jibi laraba da zasu kada kuri’ar karshe kan tsigeta domin fuskantar shari’ar ko akasin haka.

Alamomi dai sun nuna cewa, babu shaka ana iya kawo karshan mulkin Rousseff mace ta farko dake mulkin kasar da kuma fafutukar kare Demokradiya.

Magoya bayan Rousseff da suka zagaye haraban majalissar sun ta ihun Dilma ta dawo mulki.

Idan har akayi nasara tsige Rousseff, to za a baiwa Michel Temer tsohon mataimakinta, da ke rikwan kwarya, kuma babban abokin hamayarta a yanzu, daman ci gaba da tafiyar da mulki har zuwa lokacin gabatar da sabon zaben kasar a shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.