Isa ga babban shafi
Brazil

Rousseff: Venezuela ta yanke hulda da Brazil

Kasar Venezuela ta sanar da katse huldar diflomasiya da kasar Brazil sakamakon tsige Dilma Rousseff. Ma’aikatar harkokin wajen Venezuela ta bayyana tsige Rousseff a matsayin juyin mulki, inda ta bukaci jakadan ta da ke Brasilia da ya koma gida.

Dilma Rousseff ta Brazil
Dilma Rousseff ta Brazil REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Venezuela ta sanar da katse duk wata dangantaka da ta shafi siyasa da diflomasiya da Brazil.

A jiya Laraba ne Majalisar Dattajai ta kada kuri’ar tsige Dilma Rousseff kan badakalar coge a kasafin kudin kasar.

Shugabannin da aka tsige

Dilma Rousseff ita ce shugaba ta baya bayan nan da Majalisa ta tsige saboda taka doka, ganin yadda tsige shugaban kasa ke da wahala a kasashen duniya.

Fitaccen shugaban da ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka nemi tsige shi, shi ne Bill Clinton lokacin da aka zarge shi da mu’amala da Monica Lewinsky.

Sauran shugabanin da ba su samu irin wannan sa’ar ba, kuma suka rasa kujerunsu, sun hada da shugaban Venezuela, Carlos Andres Perez da shugaba Abdala Bucaram na kasar Ecuador.

Sauran sun hada da shugaba Alberto Fujimori na Peru da shugaba Abdurrahman Waheed na Indonesia da shugaba Rolandas Paskas na Lithuania da shugaba Fernando Lugo na Paraguay.

Shugabannin da aka tilastawa sauka daga kujerunsu kuma sun hada da Fernando Collor de Mello na Brazil da Ezer Weizmann da Moshe Katsav na Israila da Christian Wulff na Jamus da kuma Otto Perez na Guatemala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.