Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar Amurka na bukatar Saudiya ta yi biya diyya

Majalisar wakilan Amurka ta amince da wani kudiri da zai bai wa iyalen mutanen da suka mutu a harin ta’addancin ranar 11 ga watan Saptumba neman diyya daga Saudiya.

Shugaban Amurka Barack Obama da sarkin Salman na Saudiya abirnin Riyadh
Shugaban Amurka Barack Obama da sarkin Salman na Saudiya abirnin Riyadh Reuters
Talla

Sai dai ana ganin kudirin zai iya fuskantar adawa sosai ganin irin yanda ake dasawa tsakanin Amurka da Saudiya.

Tuni dai fadar shugaban Amurka da ke adawa da matakin ta bayyana cewa, shugaban Barack Obama zai yi amfani da matsayinsa don hawa kan kujerar na ki kan wannan niya.

Masu adawa da mataki na ganin hakan na iya kawo raunin huldar da ke tsakanin kasashen biyu

Mutane 15 daga cikin 19 da ke da hannu wajen kitsa harin a shekarar 2001 a New York da Washington ‘yan kasar Saudiya ne.

Kungiyar Al Qaida ce ta shirya harin, kuma har yanzu babu wani bincike na kasar Amurka da ya nuna cewa akwai hannun magabatan kasar Saudiya a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.