Isa ga babban shafi
Amurka

Likitan Clinton ya ce 'yar takarar na da koshin Lafiya

Likitan da ke kula da 'yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton ya gabatar da takardun da ke dauke da shaidar lafiyar ta inda ya ke cewa tana da koshin lafiyar da za ta iya gudanar da aikin shugaban kasa.

'Yar takarar Shugabanci kasa a Democrats Hillary Clinton
'Yar takarar Shugabanci kasa a Democrats Hillary Clinton REUTERS/Brian Snyder
Talla

Likitan Lisa Bardack ya ce lallai Clinton na fama da cutar sanyi da ake kira ‘pneumonia’ amma ba wadda za ta iya hana ta gudanar da harkokin ta ba ne.

Rade radi game da lafiyar 'yar takarar da kuma yadda aka dauke ta daga wajen taron tunawa da wadanda suka mutu a harin 9 ga watan Satumba ya dada jefa shakku ga Amurkawa kan halin da Clinton ke ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.