Rasha da Syria sun dakatar da kai hari a Aleppo
Rasha da Syria sun sanar da dakatar da kai hare-hare ta sama a kan birnin Aleppo, a daidai lokacin da ake fatan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita buda wuta, matakin da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai suka yi na’am da shi.
Wallafawa ranar:
Sai dai Amurka na shakku ga Rasha duk da ta yi na’am da matakin kasar na tsagaita wuta a yankin na Aleppo.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta da niyyar bai wa hukumomin agajinta damar isar da kayan jin kai ga jama’ar da ke rayuwa a Aleppo duk da Rasha da Syria sun amince su dakatar da kai hare hare.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole sai ta samu tabbaci daga bangarorin da ke rikici a Aleppo kafin ta tura kayan agaji zuwa yankin.
An nuna hotunan mutanen Aleppo saman titi suna tsintar abin da za su ci a yau Talata bayan an tsagaita wuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu