Da wuya Amurka ta cika alkawarin Paris
Wani binciken kwararru ya bayyana cewa, akwai yiwuwar Amurka ta gaza cika alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar dumamar yanayi da aka cimma a birnin Paris na Faransa da ziammar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a kasashen duniya.
Wallafawa ranar:
Wannan dai na zuwa ne bayan nasarar da Donald Trump ya samu a zaben shugabancin Amurka da aka gudanar a ranar Talata, abin da ya haifar da shakku dangane da makomar yarjejeniyar nan gaba.
To sai kwararrun sun ce, ko da Trump bai soke tsare-tasren shugaba Obama ba kan wannan batu, akwai yiwuwar Amurka ta gaza rage fitar da gurbataccen hayakin nan da shekaru 15 masu zuwa.
A cewar direktan cibiyar yaki da matsalar sauyin yanayi da ke birnin Cologne na Jamus Niklas Hohne, matsalar fitar da hayakin za ta fi tsananta a Amurka matukar Trump ya yi watsi da tsare-taseren shugaba Obama mai barin gado na rage gurbata muhalli.
Amurka dai ta yi alkawarin rage kashi 26 zuwa 28 cikin 100 na hayakin da ta ke fitarwa a yarjejeniyar da ta cimma tare da kasashen duniya a birnin Paris na Faransa a bara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu