Isa ga babban shafi
Philippines

Da kaina na ke kashe mutane- Duterte

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ya ce, da kansa ya ke kashe mutanen da ake zargi da aikata laifuka a lokacin da ya ke rike da mukamin Magajin Garin Davao.

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya kaddamar da yaki da masu safarar kwayoyi bayan zaben shi shugaban kasa
Shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya kaddamar da yaki da masu safarar kwayoyi bayan zaben shi shugaban kasa REUTERS/Lean Daval Jr
Talla

Duterte ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga tawagar 'yan kasuwa kan shirinsa na yaki da safarar miyagun kwayoyi wanda yanzu haka, ya yi sanadiyar kashe dubban mutane ba tare da an kai su gaban kotu ba.

Shugaban ya ce, a wancan lokaci da ya ke rike da mukamin Magajin Gari, da kansa ya ke kashe wadanda ake zargin don nunawa 'yan sanda yadda za suyi.

Duterte ya ce, yana hawan babur yana zagaya garin Davoa don neman fitina domin ya kashe mutane.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.