Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya sauke lasisin hako mai a tekun Atlantic da Arctic

Shugaban Amurka mai barin gado Barrack Obama ya dakatar da bayar da sabbin lasisin ayyukan hako danyen man fetur da kuma isakar gas a iyakokin kasar da ke tekunan Atlantic da Arctic.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama REUTERS
Talla

Obama ya yi amfani da wata doka ce da ta bai wa shugaban kasa damar takaita bada sabbin lasisin hakar danyen man da Iskar gas a muhallan da ake bukatar karewa daga gurbata.

Obama dai ya ce matakin na a matsayin hanyar kare muhallin daga gurbacewa da hallaka halittun da ke rayuwa a wajen saboda kwararan danyen man sakamakon ayyukan hakarsa.

Matakin na kunshe ne cikin sanarwar hadin-gwiwa tsakanin Amurka da Canada na daukar matakin haramta ba da sabbin lasisin hakar albarkatun man a iyakokinsu da ke tekunan na arctic da kuma Atlantic.

Sai dai kuma babbancin matakin kasashen biyu a nan shi ne yadda kasar Canada ta amince da sake nazari kan matakin, duk bayan shekaru biyar yayinda Amurka ta ce matakin haramcin na din-dindin ne.

A halin yanzu tilas shugaban Amurka mai jiran gado ya garzaya kotu muddin yana bukatar soke wannan mataki, ganin cewa a baya ya sha alwashin fadada ayyukan tonon albarkatun man a tekunan Arctic da Atlantic.

Masu rajin yaki da gurbatar yanayi da muhalli dai na kallon matakin a matasayin ci gaba ga fafutukar da suke yi. Kasancewar a shekarar 1989 an taba samun kwararan man cikin ruwa da ya mamaye akalla nisan sama da kilomita 1,500 tare da halaka dubban halittun ruwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.