Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta yi barazanar yin gaban-kan-ta a Syria

Kasar Amurka ta yi gargadin daukan mataki a Syria, muddin Majalisar Dinkin Duniya ta gaggara tabuka komai kan harin da aka kai da makami mai guba a kasar, wanda ya salwantar da rayukan mutane da dama ciki hada kananan yara.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ®REUTERS/Carlos Barria
Talla

Jakadiyar Amurka, Nikki Haley, ta ce a duk lokacin da MDD ta gaza jagoranci aikin tare, to hakan zai iya tilasmata yin gaban-kan-ta don daukan mataki ita guda.

Gargadin Haley, na zuwa ne a wani tattaunawan gaggawa da kwamitin tsaro na Majalisar ya gudanar kan bukatar Faransa da Britaniya, bayan kazamin harin a yankin da ‘yan tawaye ke rike da shi a Idlib.

Halley ta kuma Soki Rasha na gaza tabuka komai duk da alakantar da Syria, tare da cewa yara nawa ake son su mutu kafin Rashan ta nuna damuwarta.

Akalla mutane 72 suka mutu ciki hada yara 20, baya ga wadanda ke cikin matsanancin hali.

Harin da aka yi amfani da makami mai guba ya kasance irinsa mafi muni da ake kai wa kasar tun bayan 2013.

Britaniya da Faransa da Amurka sun gabatar da daftarain bukatar bincike, sai dai Rasha ta nuna adawarta da tsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.