Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa-Amurka-Syria

Korea ta Arewa ta ce hari da Amurka ta kai Syria shishshigi ne da babu yafiya

Kasar Korea ta Arewa ta soki kasar Amurka saboda hari da Dakarun Amurka suka kai Syria wanda Amurka ta ce ramuwar gayya ce saboda amfani da makamai masu guba da sojan Syria suka yi kan jama’a.

Hoton shugaban Korea ta Arewa  Kim Jong Un na hangen nesa da naurori yayin da yake kallon wani atasaye na soja.
Hoton shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un na hangen nesa da naurori yayin da yake kallon wani atasaye na soja. Reuters/路透社
Talla

Kalaman sun kasance irinsa na farko daga Korea ta Arewa tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci sojansa da su kai hari wani sansanin sojan Syria inda ake zaton daga nan ne aka cilla makamai masu guba da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 90.

Kamfanin Dillancin Labaran korea ta Arewa ya sanar da cewa Gwamnatin kasar na daukan harin da Amurka ta kai a matsayin ''shishshigi da ba za’a yafe ba''.

Saboda irin wannan katsalandan ne inji sanarwar ta sa Korea ta Arewa zama cikin shirin ko ta kwana.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.