Korea ta Arewa na shirye domin mayar da martani
Kasar Korea ta Arewa ta bayyana cewa mudin aka kaiwa kasar hari da makaman Nukliya ,to za ta yi amfani da nata makaman domin mayar da martini,kalaman shugaban kasar Kim Jong Un a zaman babban taron jam’iyyar dake mulkin kasar.
Wallafawa ranar:
Ana jiran sanarwa ta musaman daga shugaban kasar yayinda Wasu mutane uku da suka taba karbar kyautar Nobel ta zaman lafiya a duniya sun bukaci a sassautawa Korea ta Arewa takunkuman da kasashen duniya suka kakaba mata bayan sun ziyarci kasar.
Mutanen daga Norway da Birtaniya da Isra’ila sun ce sun gani da idonsu takunkuman sun yi tasiri matuka .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu