Isa ga babban shafi
MDD

Rasha ta hau kujerar na-ki akan Syria

Rasha ta hau kujerar na-ki a game da daftarin kudurin da kasashen Amurka, Birtaniya da kuma Faransa suka gabatar domin bayar da damar yin bincike dangane da harin da aka kai da makamai masu guba a Syria.

Jekadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vladimir Safronkov yana daga hannun yin watsi da daftari akan Syria
Jekadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vladimir Safronkov yana daga hannun yin watsi da daftari akan Syria REUTERS
Talla

Wanan ne dai karo na 8 da Rasha ke hawan kujerar na-ki a duk lokacin da aka gabatar da wani kuduri da ya shafi kasar Syria mai fama da yakin basasa.

Matakin hawan kujerar na-ki da Rasha ta dauka ya zo ne a daidai lokacin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ke gudanar da ziyarar aiki irinta ta farko a birnin Moscow, inda ya gana da shugaban Vladimir Putin bayan ganawa da takwaran aikinsa Sergei Lavrov.

Sa’o’i kadan kafin ziyarar, fadar White House a Amurka ta bayyana cewa alaka tsakaninta da Rasha ta yi tabarbarewar da ba a taba ganin irinta ko a lokacin yakin cacar baka tsakanin manyan kasashen na duniya guda biyu.

Shugaba Vladirmir Putin a wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Rasha ya bayyanar cewa, rashin yarda a tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban ciki har da bangaren tsaro, ya samo asali daga rawar da kasashen ke takawa a rikicin Syria.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, wanda ke zantawa da manema labarai bayan ganawarsa ta Tillerson a jiya Laraba a birnin Moscow, ya ce duk da wannan sabani, kasashen biyu za su ci gaba da tattaunawa domin samun fahimtar juna a tsakaninsu.

Sai dai sabanin ra’ayi dangane da rikicin na Syria, bai hana wa Rasha da Amurka yin ittifaki cewa dole ne su hada gwiwa domin yaki da ta’addanci wanda shi ne babban kalubalen da duniya ke fama da shi a wannan zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.