An kashe Kwamandan IS a Afghanistan
An kashe wani babban kwamandan mayakan IS da ke jagorantar hare-haren ta’addanci a Afghanistan, da suka hada da munmunan harin da aka taba kai wa asibiti in da mutane akalla 50 suka mutu. Hukumomin Amurka da Afghnistan ne suka tabbatar da kashe kwamandan a wani farmakin da dakarun kasashen biyu suka kai a lardin Nangarhar.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwar da fadar shugaban Afghanistan ta fitar, ta ce dakaru na musamman ne suka kashe babban kwamandan da ake kira Abdul Hasib a wani farmakin da suka kaddamar a gabashin lardin Nangerher.
Hasib shi ne kwamandan IS na biyu da dakarun Afghanistan da Amurka suka kashe a cikin watanni 9.
Kisan kwamandan na IS na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Amurka ta kai hari da wani katon bom a mabuyar mayakan na IS.
An bayyana Abu Nasib a matsayin wanda ke jagorantar hare-haren IS a Afghanistan, da suka hada da harin da aka kai a birnin Kabul a watan Maris da ya kashe mutane akalla 50.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu