Isa ga babban shafi
Amurka

Duniya ta damu da ficewar Amurka daga yarjejeniyar dumamar yanayi

Kasashen duniya sun yi tir da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na janye kasar daga yarjejeniyar rage dumamar yanayi da aka cimma a watan disambar 2015 a birnin Paris.

TRUMP-MERKEL
TRUMP-MERKEL REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Trump ya ce ya dauki wannan mataki ne lura da irin illolin da yarjejeniyar za ta haifar wa tattalin arzikin Amurka. To sai dai tsohon shugaban kasar Barack Obama da sauran manyan kasashen duniya sun yi allawadai da wannan mataki da Trump ya dauka.

A lokacin da yake sanar da wannan mataki, shugaba Donald Trump, ya ce janyewar ne mafi a’ala domin kare muradun Amurka da kuma al’ummarta.

Trump ya ce domin sauke alhakin da ya rataya a wuyana na kare Amurka da kuma al’ummarta, Amurka za ta janye daga yarjeniyar rage dumamar yanayi da aka kulla a birnin Paris. To sai dai a shirye muka mu shiga tattaunawa da sauran kasashen duniya domin yi wa yarjejeniyar ta Paris gyara ko kuma samar da wata sabuwar yarjejeniya.

To sai dai tsohon shugaban Amurka wanda ya sanya wa yarjejeniyar hannu a watan disambar 2015 Barack Obama, ya bayyana matakin da Trump ya dauka da cewa zai haifar da mummunan sakamakon ga Amurka da ma sauran kasahen duniya a nan gaba.

A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar jim kadan bayan sanarwar ta Donald Trump, kasashen Jamus, Faransa da Italiya, bayan tir da allawadai, sun ce ba za su amince a sake yi wa yarjejeniyar bita ba.

Kin amincewa da yarjejeniyar Paris dai na nufin cewa masana’antun Amurka za su ci gaba da fitar da tururi mai gurbata yanayi kamar yadda ta saba, sannan ba za ta zuba ko sisin kobo ba a asusun musamman da yarjejeniyar Paris ta bukaci a kafa ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.