Isa ga babban shafi
Faransa

Jam'iyar Shugaban Faransa Macron Na Kan Gaba A Zaben Majalisar Dokoki

Yau aka gudanar da zabukan wakilan majalisar Dokokin kasar Faransa zagaye na farko,  inda ake ganin jam'iyar Shugaba Emmanuel Macron na matukar bukatar samun rinjayen wakilai a majalisar.

Shugaban Faransa bayan jefa kuriarsa a zaben wakilan majalisar Dokokin Faransa.
Shugaban Faransa bayan jefa kuriarsa a zaben wakilan majalisar Dokokin Faransa. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Ma'aikatar Harkokin cikin gida na Faransa ta fadi cewa kashi 40.75 daga cikin dari na masu kuria suka jefa kuri'u a zaben na yau.

Tun bayan samun nasara  a zaben shugaban kasa ranar bakwai ga watan jiya bisa  abokiyar takarar sa Uwargida Marine Le Pen, Emmanuel Macron ke daukan hankulan jama’a dake son ganin yadda yake taka rawar shugabancin Faransa.

Faransa na da jimillan kujerun wakilan majalisar Dokokin 577  da suka hada da kujeru 11 na wakilai ‘yan kasar Faransa mazauna kasashen duniya.

Tuni dai Jam'iyar Emmanuel Macron ta Republic on the Move ta lashe kujeru 10 daga cikin 11 na mazauna wata kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.