Sabuwar Majalisar Venezuela ta kori mai shigar da kara
Sabuwar Majalisar Dokokin Venezuela ta kori mai shigar da kara ta kasar da ke adawa da gwamnati, Luis Ortega daga mukaminta.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne a yayin da Majalisar ta fara aikinta a yau Asabar bayan rantsar da ita a jiya Jumma’a.
Kazalika Majalisar ta kuma bukaci a gurfanar da uwargida Ortega wadda ta ce, an tafka magudi a zaben ‘yan Majalisar da aka gudanar a makon da ya gabata.
Gabanin sanar da matakin koran ta, Mai shigar da kara ta ce, jami’an sojin kasar sun yi ofishinta kawanya a birnin Caracas, in da suka hana ta shiga ofishin, sannan kuma ta zarge su da musguna ma ta.
Gwamnatin kasar ta bai wa Majalisar Dokokin mai mambobi 545 karfin sake rubuta kundin tsarin mulkin kasar, yayin da Ortega ta bukaci kotu da ta dakatar da rantsar da Majalisar saboda zargin magudi a zaben.
‘Yan adawa na ganin cewa, zaben ‘yan Majalisar wani yunkuri ne na shugaba Nicolas Maduro don ci gaba da kankamewa kan karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu