An harbe wani dan takara a Venezuela
A yayin da ake gudanar da zaben ‘yan majalisu a Venezuela mai fama da rikici da matsalolin tattalin arziki, rahotanni sun ce an kashe daya daga cikin ‘yan takarar dan majalisa.
Wallafawa ranar:
Jose Felix Pineda, wanda lauya ne kuma daya daga cikin wadanda ke gwagwarmayar sake rubuta kundin tsarin mulki, an kashe shi ne a gidansa da ke garin Bolivar kafin soma kada kuri’a.
Ana zaben ne dai cikin yanayi na fargaba da tashin hankali a Venezuela inda wasu rahotanni suka ce an kashe shugaban matasa ‘yan adawa a wani gangani adawa da zaben da ake gudanarwa a yau Lahadi.
An shafe kwanaki ana zanga-zangar kin jinin gwamnatin Nicolas Maduro, inda mutane sama da 100 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu