Isa ga babban shafi
Venezuela

Sojin Venezuela na cikin shirin ko ta kwana

Rundunar Sojin Venezuela na cikin shirin ko-ta-kwana bayan wani harin gurneti da aka yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen kaddamar da shi kan kotun kolin kasar.

Jami'an tsaron Venezuela na cikin shirin ko ta kwana bayan harin ta'addancin da aka kaddamar kan kotun kolin kasar
Jami'an tsaron Venezuela na cikin shirin ko ta kwana bayan harin ta'addancin da aka kaddamar kan kotun kolin kasar REUTERS/Isaac Urrutia
Talla

An kaddamar da farmakin ne kwana guda bayan shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya sanar da cafke wasu ‘yan adawa da ake zargi da yi wa gwamnatinsa makarkashiya da nufin share wa Amurka hanyar kutsowa cikin kasar.

Shugaba Maduro da ke yawan fadin cewa, ana shirin yi ma sa juyin mulki, ya ce, wani tsohon jami’in ‘yan sanda ne da ya taba aiki a karkashin wani tsohon ministan kasar, ya tuka jirgin mai saukar ungulu.

Shugaba Maduro ya kara da cewa, an kuma yi harbe-harben bindiga har sau 15 kan ma’aikatar cikin gidan kasar ta Venezuela a yayin wannan farmaki.

Tuni dai gwamnatin Maduro ta baza sojojinta don tabbatar da zaman lafiya a kasar kamar yadda Maduro ya bayyana a fadarsa ta Miraflores.

Sannan ya ce, ko ba dade ko ba jima, za su cafke wannan jirgin mai saukar ungulu da kuma wadanda suka kai harin na ta’addanci.

Babu dai ko da mutun guda da ya jikkata a sanadiyar harin.

A ‘yan kwanakin nan dai, Venezuela ta yi fama da zanga-zangar adawa da gwamnatin Maduro, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 76.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.