Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sha suka kan nuna ban-banci a rikicin Charlottesville

Fadar gwamnatin Amurka ta jaddada cewa, shugaban kasar Donald Trump, ya yi alla-wadai ga dukkanin bangarorin da ke da hannu a zanga-zangar wariyar launin fata da ta yi sanadiyar mutuwar wata matashiya a birnin Charlottesville na jihar Virginia.

Zanga-zanagar wariyar launin fata a birnin Charlottesville da ke Virginia
Zanga-zanagar wariyar launin fata a birnin Charlottesville da ke Virginia PAUL J. RICHARDS / AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan an zargi Trump da nuna ban-banci wajen caccakar rikicin, in da ya ki fitowa fili don yin alla-wadai kan fararen fatar da ke zanga-zangar.

Matashiyar mai shekaru 19 ta mutu ne bayan wata mota ta afka kan dan-dazon jama’ar da ke adawa da masu zanga-zangar wariyar launin fatar.

Shugaba Trump ya yi alla-wadai da lamarin ta bangarori da dama, amma an zarge shi da kin fitowa fili wajen sukar ainihin fararen fatar da ke zanga-zangar ta nuna wariyar launin.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ta fiyar, Fadar White House ta ce, caccakar Trump ta shafi dukkanin bangarorin da ke da hannu a zanga-zangar da suka hada da masu matsannancin kishin launin.

Har ila yau, shugaban ya kuma bukaci dukkanin Amurkawa su hada kansu kamar yadda fadar White ta fadi.

Manyan Mambobin jam’iyyar Republican mai mulki na daga cikin wadanda suka soki Trump kan rashin fitowa filin wajen sukar fararen fatar.

Baya ga matashiyar da ta rasa ranta a rikcin, an kuma samu mutane 19 da suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.