Isa ga babban shafi
ILO

Sama da ma'aikata milyan 2 na mutuwa duk shekara sanadiyyar aiki-ILO

Hukumar kwadago ta duniya ILO, ta ce akalla ma’aikata miliyan Biyu, da dubu dari hudu ne ke mutuwa a duniya duk shekara, sakamakon kamuwa da cutuka daban daban, a dalilin ayyukansu.Daraktan hukumar ta ILO Guy Ryder, ya bayyana haka ne a taron kwadago da ke gudana a Singapore karo na 21, kan inganta hanyoyin kare lafiyar ma’aikata yayin gudanar da ayyukansu.

Galibin ma'aikatan dai a cewar hukumar ta ILO na mutuwa ne sanadiyyar cutuka, lamarin da ke nuna cewa ma'aikatu ba su fiya mai da hankali wajen kulawa da lafiyar ma'aikatansu.
Galibin ma'aikatan dai a cewar hukumar ta ILO na mutuwa ne sanadiyyar cutuka, lamarin da ke nuna cewa ma'aikatu ba su fiya mai da hankali wajen kulawa da lafiyar ma'aikatansu. Reuters
Talla

Ryder ya ce hukumar kwadagon ta ILO, ta tattara alkaluman ma’aikatan da ke rasa rayukansu ne bayanda suka gudanar da bincike tare da hadin gwiwar, gwamnatocin Finland, Singapore, kungiyar tarayyar turai, da kuma hukumar kasa da kasa da ke kare hakkin lafiyar ma’aikata.

A cewar Ryder mutuwar ma’aiakata miliyan 2 da dubu dari hudu a fadin duniya dalilin cutukan da ke da alaka da wuraren ayyukansu, ya nuna yadda ma’aikatu da hukumomi da dama basa mayar da hankali kan yiwa tsare-tsaren kare lafiyar ma’aikatansugarambawul, wanda kuma tilas a magance wannan matsala.

Taken taron hukumar kwadagon ta duniya na wannan shekara dai shi ne Matasa da kuma tasirin inganta tsarin tafiyar da ayyukansu da kuma kare lafiyarsu.

Hukumar kwadagon ta duniya ILO ta yi hasashen cewa cikin shekarar da muke ciki kadai, akalla matasa miliyan Arba’in ne zasu fantsama neman aiki a ma’aikatu da hukumomi a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.