Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zangar kungiyoyin kwadago a Faransa

Kazamar zanga zangar nuna rashin amincewa da tsarin dokar sake fasalta ayyukan kwadago da aka gudanar a ranar laraba a kasar Faransa ta yi sanadiyyar jikkatar yan sanda 2 a yayinda mutane 124 suka shiga hannun jami’an tsaro a garuruwa da dama na kasar ta Faransa.

Bernard Cazeneuve Ministan cikin gidan Faransa
Bernard Cazeneuve Ministan cikin gidan Faransa STEPHANE DE SAKUTIN / AFP
Talla

Ministan cikin gidan kasar Bernard Cazeneuve ya bayyana kama mutane 124 a ko ina cikin fadin kasar ta Faransa, inda jimilce suka kai mutane 382 da ake tsare da su tun farkon barkewar zanga zangar ta kungiyoyin kwadago dake nuna adawa da sabuwar dokar aikin tun ranar 9 ga watan maris din da ya gabata kawo yanzu .

Sakamakon yan sanda ya bayyana yawan mutanen da suka halarci zanga zangar a birane daban daban na kasar inda a birnin Nantes aka samu halartar mutane 8500 majiyar kwadago kuma tace dubu (20.000), 5500 Havre, Lyon, 4800 Marseille, 4500 Bordeaux 4000 Rennes, kamar Rouen, 3800 à Toulouse, 3600 à Grenoble, 3000 à Tours. À Bayonne et Strasbourg, 2.500, 2.200 à Caen, 2.000 au Mans ou à Orléans.

Yan sanda dai sun ce an samu taho mugamar ne sakamakon yadda wasu masu zanga zanga 300 da suka rufe fuskokinsu ne suka afkawa jami’an tsaro da jifa da a ci balbal a zanga zanga da ta hada mutane dubu 60 a birnin paris .

Ministan cikin gidan Bernard Cazeneuve ya bukaci kungiyoyin ma’aikatan da su yi tir da masu farma jami’an tsaro tare da yin tir da allah wadai da yadda ake ci gaba da ingiza wutar rikici a kasar da sunan nuna rashin amincewa da tsarin dokar kwadagon da gwamnatin yan gurguzun ke son samarwa a kasar da ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar tada kayar bayan kungiyoyin kwadago a nahiyar turai.

Sakamakon yan sanda dai ya ce gaba daya mutane dubu 150 ne suka halarci zanga zangar ta RANAR laraba a yayinda kungiyoyin kwadago ke cewa dubu 500 a ko ina cikin fadin kasar ta Fransa

a jimilce dai mutane miliyan 1,2 suka halarci zanga zangar tun farkon barkewar a ranar 9 ga watan maris din da ya gabata a cewar kungiyoyin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.