Isa ga babban shafi
Mexico

Ana ci gaba da aikin ceto a girgizar kasar Mexico

Masu aikin agaji na ci gaba da neman mutanen da ke da sauran nimfashi da buraguzan gine-gine suka danne bayan aukuwar mummunar girgizar kasa mai karfin maki 7.1 a Mexico, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 200.

Sama da mutane 200 sun mutu a girgizar kasar Mexico
Sama da mutane 200 sun mutu a girgizar kasar Mexico REUTERS/Ginnette Riquelme
Talla

Jami’an kashe gobara da 'yan sanda da sojoji da kuma masu aikin sa-kai, sun shafe tsawon yinin jiya suna gudanar da aikin ceto.

Girgizar kasar ta shafi wata makarantar kananan yara, in da aka tabbatar da mutuwar yara 21, yayin da wasu suka bace, amma masu aikin ceton sun yi nasarar ceto yara 11 tare da malaminsu guda bayan kwashe sa'oi 24 a karkashin kasa.

Shugaban agajin gaggawa Luis Felipe Fuente ya ce, ya zuwa yanzu mutane 230 aka gano gawawakinsu, yayin da aka kaddamar da zaman makoki na kwanaki 3.

Sai dai a wani sako da ya aike da kafar sada zumunta ta Twitter, shugaban Mexico, Enrique Pena Nieto ya gargadi cewa, adadin mamatan na iya karuwa nan gaba.

Ba a karon farko kenan ba da ake samun mummunar girgizar kasa da ke lakume rayukan mutane da dama a Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.