Isa ga babban shafi
Mexico

Tawagar jami'an Isra'ila za ta fara aikin ceto a Mexico

Wata tawagar Isra'ila ta mutum 70 da ta kunshi dakarun soji da Injiniyoyi za ta  fara aikin ceton rai yau Mexico baya da adadin mutanen da girgizar kasa ta kashe ya haura sama da mutum 200. Firaministan Isra'ila Bejamin Netanyahu ya ce dakarun za su isa don bayar da agaji ga wadanda mummunar girgizar kasar mai karfin maki 7.1 ta afkawa kasar.

Har yanzu dai ana ci gaba aikin ceton rayukan wadanda baraguzan gine-gine ya rufe su, yayinda iyaye da dama ke cikin fargabar halin da yaransu suke ciki baya da aka gaza gano kimanin yara 21 da makarantarsu ta rufta.
Har yanzu dai ana ci gaba aikin ceton rayukan wadanda baraguzan gine-gine ya rufe su, yayinda iyaye da dama ke cikin fargabar halin da yaransu suke ciki baya da aka gaza gano kimanin yara 21 da makarantarsu ta rufta. Reuters
Talla

A cewar kakakin yada labaran rundunar sojin Isra'ila Jonathan Conricus, tawagar jami'an ta tashi daga kasar tun da misalin karfe uku na yammacin yau Laraba kuma za ta isa Mexico cikin sa'o'i 18 masu zuwa.

Tawagar ta mutum 70 ta kunshi Injiniyoyi 25 da za su gudanar da aikin duba gine-ginen yankunan da ke fuskantar ibtila'in guguwar don tabbatar da nagartarsu tare da ganin basu fuskanci matsala ba.

Masu aikin ceto a Mexico dai sun tsananta bincike tun a safiyar yau Laraba, don ceto rayukan mutanen da ke da sauran lumfashi a baraguzan gine-ginen da girgizar kasar ta rusa cikin daren jiya Talata, baya da a jiyan suka raba dare wajen aikin ceton.

Ilahirin mahukuntan kasar dai hankalinsu ya tafi kan wata makarantar yara da ke tsakiyar kudancin birnin da ta rufta inda aka gano gawakin yara 21 baya ga manya 5 a baraguzan gine-ginen, yayinda kuma ake ci gaba da neman akalla yara 30 da malamansu da suka bace.

Daruruwan jami'an soji da masu aikin agaji ne suka raba dare wajen ganin sun ceto wani malami da dalibansu 2 dake karkashin gini da aka gano suna raye.

Wata Mata Adriana Fargo da ta ja tunga a wajen baraguzan ginin don sanin halin da 'yar mai kimanin shekaru 7 ke ciki ta shaidawa manema labarai cewa tana cikin rudani anin cewa har yanzu ba a kai ga gano yarinyarta ba.

Shugaban kasar Enrique Pena Nieto wanda ya ce kai ziyara wajen faruwar lamarin ya ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa nan gaba la'akari da yadda har yanzu ba a kai ga gano inda wasu suka shige ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.