Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya mayar da martini kan kalaman Kim Jum-Un

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-Un da cewa zai yi nadamar da bai taba yi ba kan zafafan kalaman daya jefe shi da su. Gargadin shugaban Amurkan na matsayin martini ga kalaman da shi Kin Jong-Un ya yi na bayyana Trump a matsayin mai fama da tabin hankali.

A cewar shugaban na Amurka, takwaransa na Korea ta arewa Kim Jung-Un baya damuwa da halin da al'ummar kasarsa ke ciki.
A cewar shugaban na Amurka, takwaransa na Korea ta arewa Kim Jung-Un baya damuwa da halin da al'ummar kasarsa ke ciki. Reuters
Talla

A martinin na Trump wanda shi ma ya bayyana Kim Jong-Un a matsayin mai tabin kwakwalwa ya ce tabbas zai dandana kudarsa kuma zai yi nadamar da bai taba yi bat un bayan fara takaddama tsakaninsu.

Da safiyar yau ne dai Kim Jong-Un ya ce akwai bukatar a duba lafiyar shugaban na Amurka Donald Trump bisa ga kalaman da yayi yayin jawabinsa a zauren majalisar dinkin duniya, baya da ya yi alkawarin murkushe kasar ta Korea ta Arewa.

A cewar shugaba Kim, Trump ya muzanta shi ya kuma muzanta kasar sa a idon duniya, yana mai cewa tabbas Trump zai ji a jikinsa inda ya bayyana kalaman na shi a matsayin haushin kare.

Sai dai kuma a martinin na Trump ya ce babu shakka ya tabbata Kim din na da tabin hankali ganin yadda bai damu da halin yunwa da talaucin da al’ummar kasar sa ke ciki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.