Isa ga babban shafi
Lafiya

Gurbacewar Muhalli ta kashe Mutum miliyan 9

Wani rahoto ya yi kiyasin cewa mutane miliyan 9 suka rasa rayukansu sakamakon gurbacewar iska a duniya cikin shekara ta 2015.

Gurbacewa Iska na lakume rayuka a duniya
Gurbacewa Iska na lakume rayuka a duniya 路透社照片
Talla

Rahotan da Mujallar, The Lancet Medical, ta wallafa ya ce kashi 92 cikin 100 na wadanda ke mutuwa marasa hali ne.

Mujallar ta kiwon lafiya ta ce Kusan rabin wadanan alkallumar sun fito ne daga kasashen India da China.

Rahotan ya kuma ce kasashen da ke da tarin masana’antu irinsu India da Pakistan da China da Bangladesh da Madagascar da Kenya, gurbacewar muhalli na sanadi rai mutum guda duk cikin mutum 4.

Karti Sandilya, jami’a a wata kungiyar kare muhalli, Pure Earth, ta ce gurbacewar muhalli da cututukan da ya ke haddasawa sunfi illar ga talakawa masara karfi da gata.

Jami’ar ta kuma bayyana cewa hakan, ba karamin barazanar ba ce ga hakkin bil’adama, na ‘yancin rayuwa da lafiya da walwala kazalika kare ‘ya’yansu daga illar da hakan ke haifarwa.

Yayin da ake kiyasta tafka asaran dala triliyan kusan 5 kowacce shekarar saboda matsalolin gurbatar muhalli, masana na cewa hakan na kuma tasiri ga ci gaban kasashe masu tasowa.

Binciken masanan ya kuma nuna cewa, Kasashe masu karamin karfi na asaran kusan kashi 9 cikin 100 na kudadden da suke samu kan cututukan da gurbacewar muhalli ke haddasawa.

Cututuka da suka shafi ciwon zuciya da shanyewar jiki da Sankara da matsalar numfashi gurbacewar muhalli ko iska ke haifar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.