Isa ga babban shafi
Amurka

Direbar Motar ya hallaka mutum 8 a Amurka

Wani Direbar motar daukar kaya ya hallaka mutane 8 lokacin da ya afkawa masu tafiya a gefen hanya, kafin ya yi karo da wata motar daukar 'yan makaranta a Manhattan da ke New York, a kasar Amurka.

Wani direbar ya kashe mutane a Manhattan
Wani direbar ya kashe mutane a Manhattan ©REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Bayanai sun ce wasu mutane 11 sun samu raunuka a harin kusa da wata makarantar da dalibanta ke shirin bikin Halloween tare da iyayen su.

Magajin Garin Birnin New York Bill de Blasio ya bayyana harin a matsayin na ta’addanci, yayin da kafofin yada labarai suka bayyana wani Dan assalin kasar Uzbekistan da ke zama a Florida a matsayin wanda ya kai harin.

Shugaba Donald Trump ya bayyana takaicin sa da harin, inda ya ke cewa ba za su bari mayakan ISIS su sake samun wurin zama a Amurka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.