Isa ga babban shafi
Amurka

Dan bindiga ya bude wuta a Sutherland

Wani dan bindiga jar fata ya buda wuta akan masu ibada cikin mujami’a a Sutherland Spring da ke jihar Texas na kasar Amurka inda ya kashe mutane 26 tare da raunata wasu fiye da 20 a jiya lahadi.

Mujami’ar  Sutherland Spring da ke jihar Texas a Amurka
Mujami’ar Sutherland Spring da ke jihar Texas a Amurka MAX MASSEY/ KSAT 12/via REUTERS
Talla

Yan Sanda sun killace unguwar ,masu bincike sun soma aiki nan take domin tanttance maharin.

Maharin wanda aka bayyana cewa shekarunsa sun haura 20, kuma ga alama sojin saman Amurka ne.

Daga bisani dai ‘yan sanda sun bayyana cewa maharin ya mutu, kuma an tarar da bindigogi da dama a cikin motarsa bayan faruwar wannan lamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.