Yawan masu kamuwa da Maleriya sun karu-WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce sama da mutane dubu 445 ne suka rasa rayukansu a fadin duniya cikin shekarar 2016, sakamakon kamuwa da cutar ta zabbabin cizon sauro.
Wallafawa ranar:
Rahoton hukumar ya ce an samu karuwar yawan wadanda ke kamuwa da cutar cizon sauron da akalla mutane miliyan biyar, daga mutane miliyan 211 da bincike ya nuna cutar Maleriya ta shafa a shekarar 2015
Bayanin rahoton ya tabbatar da cewa miliyan 57 da dubu 3 da cutar da addaba sun fito ne daga Najeriya kadai.
WHO ta ce a halin yanzu ana bukatar ware sama da akalla dala biliyan 6 da dubu 500 nan da zuwa shekarar 2020, domin kawo karshen cutar cizon sauro a shekarar 2030.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu