Isa ga babban shafi

Trump ya yi mummunar suka kan kasashen China da Rasha

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi mummunar suka kan kasashen China da Rasha wadanda ya bayyana su a matsayin kasashen da ke nema dakile ci-gaban manufofin Kasar sa.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Yuri Gripas
Talla

A jawabin da ya yi na farko kan manufofinsa na tsaro, a karkashin shirin sa na Amurka farko, Trump ya zargi Rasha da China a matsayin wadanda ke kalubalantar ci-gaban Amurka da karfin fada aji a duniya da matakan tsaron da ta ke dauka.

Trump ya bayyana nukiliyar Rasha a matsayin babbar barazanar da Amurka ke fuskanta, yayin da kasar ke ci gaba da yada ikon fada ajin ta zuwa kusa da iyakokin Amurka domin rage mata karfi.

Shugaban ya bayyana shirin fadada karfin fada ajin Amurka da kuma murkushe ‘yan ta’adda tare da duk wanda ke yi wa kasar sa barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.